Daga: Abbas Yakubu Yaura
Tsohon mataimakin gwamna a tsohuwar gwamnatin APC a jihar Bauchi, Audu Sule Katagum tare da kwamishinoni da wasu mukarrabansa, sun ziyarci gwamna Bala Mohammed a gidan gwamnati da ke Bauchi a ranar Alhamis inda suka bayyana ficewarsu daga APC zuwa jam’iyyar PDP.
Gwamna Bala wanda ya karbi masu sauya shekar tare da nuna jin dadinsa da ganin sun cancanci ficewa daga tsohuwar jam’iyyarsu zuwa jam’iyyar PDP mai mulki a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-duminsa: Atiku Ya Nada Dino Melaye, Daniel Bwala A Matsayin Masu Magana Da Yawunsa
Da yake mayar da martani game da ci gaban, Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Hamza Koshe Akuyam ya yi maraba da wadanda suka sauya sheka zuwa PDP tare da nuna kwarin gwiwar cewa zuwan nasu zai kara wa jam’iyyar nasara a babban zaben shekara mai zuwa a jihar.
“Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya nuna mana wannan rana mai cike da tarihi a gare mu, kuma tana da matukar ma’ana a gare mu a matsayinmu na jam’iyyar PDP a jihar Bauchi.”
A Wani Labarin Kuma Kungiyar malaman jami’o’in ASUU reshen jihar Kaduna (KASU) ta ki komawa karatu duk da barazanar da gwamnan jihar Nasir El-Rufai na korar su.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, hukumar gudanarwar makarantar ta bukaci daliban da su koma karatu domin jarrabawar su bayan barazanar da gwamnan ya yi na korar su.
Dangane da abubuwan da suka gabata, an ga wasu daga cikin daliban a ajujuwa suna rubuta jarabawarsu a ranar Litinin karkashin kulawar shugaban jami’ar da sauran ma’aikatan cibiyar.
Majiyar jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa , mambobin kungiyar malaman jami’o’i na kasa wato (ASUU) reshen jami’ar sun ki shiga cikin aikin kulawar, su na masu cewa, yajin aikin na ci gaba da gudana don haka ba za su shiga aikin jarrabawar ba.
Rahotanni sun bayyana cewa, kungiyar a wata sanarwa da ta fitar a karshen taronta a jami’ar Kaduna da ya gudanar a ranar Litinin din da ta gabata, ta ce an samu kura-kurai a lokacin jarrabawar.
Shugaban kungiyar ASUU – reshen KASU, Kwamared Peter Adamu da Comrade Usman Abbas, sakataren kungiyar ne suka sanya wa sanarwar hannun.
Duk da haka Sanarwar ta yi kira ga ƙungiyar da ta tattara dukkan laifuffukan da aka samu a cikin jarrabawar da aka yi sannan a tura su ga hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa.
A nasa martanin, Shugaban Jami’ar Farfesa Abdullahi Ashafa, ya ce, kungiyar ASUU reshen Jami’ar na goyon bayan Jami’o’in Tarayya ne kawai, Amma ba su da wata matsala kai tsaye da Gwamnatin Tarayya da ya jawo yajin aikin.