By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon ministan kwadago Alhaji Hussaini Zanwa Akwanga ya rasu.
Akwanga, ya rasu ne a ranar Juma’a, yana da shekaru 77 bayan ya yi fama da rashin lafiya a kasarsa Akwanga, hedikwatar karamar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.
Tsohon Ministan,kafin rasuwar dai ya kasance kwararren malami, ya zama minista a shekarar 2003 amma shugaban kasa na wancan lokacin Olusegun Obasanjo ya kore shi daga mukaminsa.
A shekarar 2017, an yi garkuwa da tsohon ministan a gonarsa dake kauyen Kurmin Tagwaye, kusa da Akwanga, amma bayan kwana biyu an sake shi bayan ya biya kudin fansa.
Mataimakin shugaban karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa, Alhaji Safiyanu Isa wanda ya tabbatar da rasuwar tsohon ministan yace “tsohon ministan ya rasu ne a yau ( Juma’a), a Akwanga”
Tuni dai aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garinsu na Akwanga.