Wani mutum a kudu maso gabashin kasar Faransa ya dalla wa shugaban kasar Emmanuel Macron mari bayan da ya kai wata ziyarar aiki.
Wani bidiyo dake ta yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda Macron ke tattaki a wani kauye dake birnin Valencd.
Mutumin ya sharara wa Macron mari ne gabannin jami’an tsaro su gaggauta janyo shi gefe.
Kuma tuni aka chafke mutane biyu da hannu kan wannan aika-aika.
Yayin da mutumin ya sharara marin, nan da nan wasu mutane suka ɓuge da ihun “ba ma bukatar akidar Macron”
A halin da ake ciki yanzu haka shugaba Macron na can yana ci gaba da gudanar da ziyarar ayyuka.