Alkalin alkalai na kasa (CJN), mai shari’a Ibrahim Muhammad zai rantsar da mai shari’a Salisu Garba a matsayin mukaddashin babban Jojin babban birnin tarayya Abuja (FCT).
Daraktan watsa labarai, majalisar shari’a ta kasa (NJC) Soji Oye, ya ce, a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Talata, cewar za a rantsar da mai shari’a Garba a kotun kolin Abuja, da misalin karfe 2 na ranar Laraba.
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da rantsar da Hon Justice Garba a matsayin mukaddashin babban Jojin babban birnin tarayya Abuja, biya bayan ritayar Hon. Justice Ishaq Usman Bello a ranar Talata.
KARANTA WANNAN: NYSC: Matasa masu yi wa kasa hidima 731 sun kamu da cutar COVID-19
Justice Garba zai ci gaba da zama a matsayin mukaddashi har zuwa ranar da majalisar dattijai za ta amince da nadin sa a matsayin babban jojin babban birnin tarayyar.
A wani labarin, Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce ba ta ƙaddamar da shirin ɗaukar aiki na sabbin ma’aikata ba.
A cewar wata sanarwa daga jami’in hulda da jama’a na hukumar, Peter Afunanya, Ph.D, dole ce ta sa hukumar fitar da wannan sanarwa biyo bayan saƙonnin bogi da ƴan damfara ke aikawa mutane na cewar hukumar DSS ta fara shirin ɗaukar aiki.
“Ya zama wajibi jama’a su sani cewa babu wanda ake karbar kudinsa idan za a dauke shi aiki a hukumar DSS.”
Haka zalika, Afunanya ya ƙara da cewa, “ana daukar aiki a hukumar ne ta hanyar tantancewa, da kuma cancanta amma ba wai ta hanyar karbar kudaden mutane ba.”