By Abbas Yakubu Yaura
Kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka a ranar Juma’a ta dakatar da kasar Burkina Faso daga cikin kungiyar sakamakon juyin mulkin da aka yi, amma bata kakabawa wasu takunkumi ba har zuwa yanzu, in ji wani mahalarta taron kolin.
Kungiyar ta ECOWAS tana kuma kira ga sabuwar gwamnatin mulkin sojan da ta saki hambararren shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore da wasu jami’an da aka tsare a lokacin juyin mulkin na ranar litinin, majiyar ta kara da cewa kungiyar zata sake gudanar da wani taro a Accra a ranar 3 ga watan Fabrairu.
Idan dai ba’a manta ba Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a ranar 27 ga watan Janairu mahukuntan soji na Burkina Faso suka hana wasu ministoci ficewa daga kasar tare da rufe iya kokin kasar.
Comments 1