• Gwamna Ganduje ya amince da Wanda zai gaji Muhuyi Magaji .
• Sakataran Yada labarai na Gwamna Ganduje, Abba Anwar ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis.
• Nadin zaifara aiki ne a nan take kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya amince da Barista Mahmoud Balarabe, a matsayin Shugaban hukumar amsan koken al’uma, da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar wato PCACC.
Babban sakataran Gwamna Ganduje a kan kafafen yada labarai Abba Anwar ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanar wa da ya fitar a yau Alhamis, a garin Kano.
“Amincewar zai fara aiki ne nan ta ke, inda ya umarci Mukaddashin hukumar da ya mika ragamar gudanarwar hukumar a nan ta ke ga Wanda zai gada mukamin” a cewar sanarwar.
Har kafin wannan sanarwar, Balarabe shine Daraktan na sashin tsare masu laifi, a ma’aikatar shari’a ta jihar Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalissar dokokin jihar Imo ta dakatar da Yan majalisu 6, an harbe harbe
Kazalika zai gaji Muhuyi Magaji Rimin Gado, Wanda majalissar dokokin jihar ta dakatar da shi a makon da ya gabata, bisa kin amincewa da wani mataki da gwamnatin jihar ta dauka a kan hukumar ta shi.
Jaridar DAILY Trust ta ruwaito cewa, an dakatar da Barista Rimin Gado ne, domin bai wa kwamitin yaki da cin-hanci da rashawa ta majalissar dokokin jihar, damar gudanar da bincike na rashin da’a, da ake zargin sa da shi, a hukumar.