Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Matawalle ya yi hijira daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP inda ya yi zango a jam’iyya mai ci ta APC.
Da ma dai tun a baya an sha rade-radin cewa Matawalle zai bar PDP, inda yanzu za a iya cewa hasashen da aka jima ana yi yabtabbata Kenan.
Mai taimakawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan kafafen sada zumunta Bashir Ahmad shine ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook a sanyin safiyar yau Lahadi.
“To yanzu Zamfara ita ma ta dawo gida kenan? Muna maka maraba Matawalle”
A ranar talata ne ake sa ran Matawalle zai sanar a hukumance hadewarsa da APCn.
Daga cikin wadanda ake hasashen sauya shekara su zuwa APC har da gwamnan Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad.