• Hukumar Kula da aiyukan Yan sanda ta ki amincewar da karawa Ibrahim Magu mukamin da akayi.
• A dai yau Alhamis ce, hukumar ta fitar da sanarwar kin amincewar.
• Ibrahim Magu dai tsohon Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ce wato EFCC.
Daga Usman Salisu Gurbin Mikiya
Hukumar Kula da Harkokin Yansanda wato-PSC a ranar Alhamis, taki amincewa da karawa tsohon Shugaban Hukumar yaki da cin Hanci da rashawa Ibrahim Magu Mukami, zuwa Mataimakin Sufeto-Janar na Yansanda.
Hukumar tace tana jiran takardar da aka wanke Magu, daga ofishin Ministan Shari’a na Kasa da kuma Sufeto-Janar na Yansandan Kasar akan zarge-zargen da ake yi mashi.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Hukumar Ikechukwu Ani ya fitar, inda ya rarrabawa Manema Labaru.
KARANTA WANNAN LABARIN: Babbar magana: An cafke mataimakin kwamishinan ƴan sanda a Kano
Jaridar Dimokradiyya ta baku rahoton wata jita-jita data futo kwanaki Kadan da suka wuce,cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na yunkurin karawa Magu Mukami duk da zarge-zargen da ake yi mashi na almundahana a lokacin da yake Jagorantar EFCC.
Comments 1