Majalisar Dattijan tarayya ta sanya kafa ta yi fatali da bukatar da aka mika mata ta amincewa da nadi Lauretta Onochie a matsayin shugabar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC.
Wannan ya watsi da majalisar ta yi dai ya biyo bayan tarin kururuwa ne da mambobin majalisar suka yi musamman yan jam’iyyar adawa da ma Kungiyoyin kare hakkin jama’a, kan cewa Onochie cikakkiyar Ƴar jam’iyyar APC ce mai mulki.
Da ma dai tun a farko tsohon shugaban hukumar ta INEC Farfesa Attahiru Jega ya gargadi shugaba Buhari da kada ya kuskura ya nada Onochie a matsayin shugabar hukumar.
Idan za a iya tunawa a watan Oktoban bara ne da shugaba Buhari ya mika sunan Lauretta Onochie a gaban majalisar kan cewa ta amince da nadin ta a matsayin shugabar hukumar INEC.
Ko da yake a ranar Alhamis Misis Onochie yayin gabatar da kanta gaban majalisar, ta musanta zargin da ake mata kan cewa tana da jam’iyyar siyasa.
Kazalika ta ce tun da shugaba Buhari ya dare kan karagar mulki a wa’adi na biyu ta tsame hannunta kwata-kwata daga harkokin siyasa don jan girmanta.