• Mutum daya ya baƙunci lahira a sabon harin Kaduna.
• Yan bindiga sun kai sabon harin ne a kauyen Anguwan Gagere da ke karamar hukumar Birnin Gwari.
• Sun Kuma yi awon gaba da Shanu sama da hamsin da Mutum bakwai da suka hadar da : mata uku. Kamar yadda wani mazaunin yankin ya tabbatar.
Yan bindiga sun kashe mutumin kauye da kuma garkuwa da akalla Mutum bakwai, da suka hadar da: mata uku, a karamar hukumar Birnin Gwari dake jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne a kauyen Anguwar Gajere dake yanki Kutemashi, na karamar hukumar a jiya Asabar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Yan bindigan, sun kuma saci Shanu sama da hamsin a kauyen.
Wani mazaunin yankin Mai suna Mohammed Birnin Gwari ya bayyana wa Jaridar Daily Trust ta wayar salula cewa, Yan bindigan sun afka yankin ne da Babura da musalin karfe daya na dare.
“Mata uku da Maza hudu Yan bindigan suka sace, tare da Shanu sama da hamsin, da kuma kashe wani mutum daya” inji Mohammadu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tattalin arzikin mu zai dawo Kuma zai cigaba da bunkasa~ Sanata Uba Sani
Tsohon Kansila yankin Mai suna Adamu Kutemashi, ya tabbatar da afkuwan lanarin.
Sai dai haryanzu rundunar yan sandan jihar Kaduna, ba ta tabbatar da afkuwar lamarin ba, bayan jami’in Hulda da jama’a na rundunar reshen jihar ASP Jalige Mohammed ya yi alkawarin, zai bada cikakken bayani, da zaran ya samu daga yankin.
Comments 1