Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatarwa majalisar dattijai da sunayen tsofaffin hafsoshin tsaro da kuma shugaban rundunar tsaro ta kasa domin nadasu a matsayin jakadun da ba na aiki ba.
Mai tallafawa shugaban kasar na musamman ta fuskar watsa labarai, Chief Femi Adesina ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Alhamis.
A cikin wasikar da ya aikewa shugaban majalisar dattijan Ahmad Lawan, Shugaban kasar ya ce: “Bisa sahalewar sashe na 171 (1), (2), (c) da kuma karamin sashe na (4) na dokokin kasa na 1999 na kasar Nigeria kamar yadda aka sabunta, Ina amfani da wannan dama domin gabatar maku da sunayen mutane biyar da ke kasa domin amincewar majalisar a nada su jakadu ba na aiki ba.
A cewar sanarwar, “Wadanda za a tantance sune: Gen Abayomi G. Olonisakin (mai ritaya), Lt Gen Tukur Y. Buratai (mai ritaya), Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), Air Marshal Sadique Abubakar (mai ritaya), da kuma Air Vice Marshal Mohammed S. Usman (mai ritaya).
“Shugaban kar na bukatar majalisar da ta duba yiyuwar amincewa da wadannan nade nade cikin gaggawa.”
Idan za a iya tunawa, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 26 ga watan Janairu, ya amince da takardun ajiye aiki na tsofaffin hafsoshin tsaro na kasar, tare da amincewa da nada wasu sabbi.