Bala Batex ya rasu ne yana da shekaru 64.
Wani daga gwamnatin Jahar Kaduna ya tabbatar ma Jaridar Daily Nigeria da rasuwar sa.
Marigayi Bala, ya rike mataimakin gwamnan Jahar Kaduna a tsakanin 2015 zuwa 2019 inda yayi murabus don takarar Dan majalisa.
KARANTA:-WATA SABUWA:- Yan majalisu za su sauke shugaban Kasa ko gwamna idan ya sauya sheka
Ya bayyana haka ne a wata takardar jajen daya baiwa manema labarai, Gwamna Elrufai ya jajenta mutuwar tsohon mataimakinsa, ya siffantashi da aboki kuma dan’uwa.
Elrufai “hakika nayi rashin dan’uwa kuma abokin aiki.”
“A cikin wannan yanayi, na sami sakon mutuwar abokina Barnabas Yusuf Bala (Bantex).
“Tun lokacin da muna Jami’a, a 1970’s har zuwa wajan aikinmu na gine-gine, sannan kuma abokin aiki a shugabanci., Bala Bantex mutum ne mai hazaka da jajircewa.
“Yayi imani da cigaban jahar mu, tare da hadin kan Al’umma domin cigaba.” Kamar yadda Elrufai ya bayyana.
Ya cigaba da cewa “Munyi nufin kawo sauyi a Siyasa da shugabancin jahar Kaduna a 2015.”
Kamar yadda gwamnan yace Bala Bantex Yana da buri da manufa wajan ciyar da Jahar gaba, duk da yanayin yayi tsamari.”
“Bala Bantex yayi aiki don cigaban jahar Kaduna a fannoni da dama, musamman lokacin da yake mataimakin gwamna.”
“Zamu rasashi matuka da kuma jajircewarsa ga Jahar Kaduna.”
“Nayi magana da iyalinsa don mika sakon ta’aziyyan gwamnatin Jahar Kaduna da ma Al’ummar jahar baki daya, za kuma mucigaba da bibiyan iyalansa duba da irin jajircewarsa akan Jahar har lokacin da lafiya.”
“hakika mun albarkantu tare da aiki da Bantex”
Ya kuma yiwa Bala Bantex addu’ar Allah ya jikanshi ya baiwa matansa da yaransa hakurin jure rashin.