• Tun safiyar jiya Talata ce ake ta, yada hotunan jaruman Kuma ake cewa sun yi aure.
•Jaridar Dimokuradiyya ta zanta da mutan biyu.
• Kuma kowa ya bayyana na shi ra’ayin dangane da lamarin.
Daga Mukhtar Yakubu.
Tun safiyar jiya labari da kuma hotunan fitattun jarumai Alhaji Hamisu Lamido Iyantama, da na Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a, suka cika dandalin sada zumunta tare da labarin za su yi aure.
Farkon labarin dai ya samo asali ne daga dora hoton da jarumar ta yi a shafin ta na Instagram, wanda hakan ya ba da damar yada hotunan, da labarin har aka yi kwaskwarima, da kuma kara wa labarin gishiri.
Domin jin gaskiyar yadda labarin ya ke dai mun ji ta bakin dukkan su Hamisu Lamido Iyantama, tare da ita Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a din.
KARANTA WANNAN LABARIN: Barayin waya sun kashe mutun 2 a jihar Kogi
Inda, da farko Rashida ta bayyana mana cewar “Gaskiya ba haka abin ya ke ba, wani fim ne Hamisu Lamido Iyantama zai yi to ina daga cikin Jaruman da za su fito a ciki, to a wajen shirye-shiryen aikin ne, muka yi wannan hoton, shi ne su kuma suka dauka suka rinka Kara labarin suna yada shi, amma dai gaskiya ba wata maganar aure a tsakanin mu, domin Hamisu Lamido Iyantama yayana ne, kuma mai gidana ne a cikin harkar fim, don haka akwai alaka mai karfi a tsakanin mu. ‘
Shi ma jarumi kuma Furodusa Hamisu Lamido Iyantama da muka tambaye shi cewa ya yi, “wannan labarin da ka gani Dirama ce ba gaskiya ba ne, kawai dai an dauki labarin an yada shi ne.”
Comments 1