Yayin da ƴan Najeriya lungu da sako ke bayyana ra’ayinsu game da salon jagorancin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wata matashiya mai suna Zainab ta bi sahun yan kasar wajen bayyana nata ra’ayin.
Kawo yanzu dai miliyoyin yan Najeriya ne ke sukar salon mulkin na shugaban kasa, ko da yake a hannu guda akwai wasu miliyoyin dake nuna son Barka.
Ita ma dai matashiyar a wani sako da ta wallafa a shafin ta na Koo wanda shafi ne da ya maye gurbin na tuwita a gurin yan Najeriya, ta ce a yanzu haka da a bata naira miliyan daya gara ta kashe Ƙwarƙwatan idanunta da murmushin shugaban lasa Muhammadu Buharin.
Ko da yake ba ita ce mutum na farko da ya fara bayyana irin wannan ra’ayi ba, amma wasu jama’a sun sanya maganar tata a mizani a matsayin wani shaguɓe.
To sai dai a hannu guda wasu mutane na ganin matashiyar ta yi ne don raha, duk da cewa al’umma a kasar nan ma cewa sun gamsu da salon mulkin shugaba Buhari, musamman a yaƙi da yan kungiyar Boko Haram.
Kawo yanzu dai daruruwan mabiya Zainab ne suka yi mata caaa a shafin na Koo, inda suke bayyana mata ra’ayoyin su mabanbanta.