Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano.
Daya daga cikin shugabannin masana’antar fina-finai ta Kannywood, kuma sakatare a kungiyar kwararru ta masu shirya fim ta kasa MOPPAN Salisu Muhammad Officer, ya bayyana harkokin da su ke gudanarwa a masana’antar ta su, da cewar duk abu guda ne da abubuwan da Malamai su ke yi, don haka a daina yi musu wani kallo na daman.
Salisu Muhammad Officer ya Kara da cewar “Idan har Malamai za su yi zagi da fadar abin da suka ga dama kuma a dora shi a YouTube, to bai kamata su ma ‘yan fim a ga laifin su ba, domin kamar yadda yan fim su ke neman suna haka su ma Malaman nan su ke neman suna”
Ya Kara da cewar “Duk irin zagin da a ke yi a kan yan fim bai taba jin wani Malami ya zo ya yi suka a kan hakan ba, don haka abin da ya kamata ‘Yan Fim su yi shi ne, su yaba wa Shugaban Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Malam Ismaila Na’abba Afakallahu, saboda kokarin da ya ke yi na kawo gyara a kan harkar fim, maimakon a ga laifin sa ya kamata ne a Goya masa baya, domin Gwamnatin jihar Kano ce ta dauke shi aiki domin ya kawo gyara ga masana’antar, a don haka bai kamata mu rinka yakar sa ba. ” in ji Salisu Muhammad Officer.
Comments 1