Daga Ibrahim Hassan Hausawa
Al’umma yanzu haka sun shiga cikin cikin wani hali na rashin tabbas, sakamakon yadda babban bankin kasa CBN ya dage cewa babu batun karin wa’adi.
Masu karbar tsofaffin kudi hakan ya sanya suka dakatar da karba, yayin da kuma a gefe guda suka shiga farautar sabbin, duk da karancin da suke yi wajen samu.
KU KARANTA: Abinda Thiago Silva Ba Zai Manta Da Shi A Chelsea Ba
A baya dai wasu gwamnoni irin na jihohin Kano, Niger da sauran su, sun bayar da umarnin kada wani dan kasuwa yaki karbar tsohon kudi, tare da daukar tsauraran hukunce hukuncen kan duk wanda ya bijirewa hakan.
To sai dai a zagayen da DIMOKURAƊIYYA ta gudanar a wasu yankunan jihar Kano, da suka haɗar da Titin gidan Zoo, Titin Gwarzo, Kasuwar Tarauni, da sauran su, ta iske yadda wasu daga cikin gidajen mai suke daɗe da bujirewa karbar tsohon kudin.
Yayin da matakin gwamnatin Kano kan hakan ya gaza haifar da ɗa mai ido.
Yanzu haka dai masu kantuna da sauran kayayyakin bukata sun daina karbar tsohon kudin tun a daren yau.
Daidai lokacin da ake dakon hukuncin kotun koli kan wannan dakatar da kudi, bayan da wasu gwamnoni suka shigar da kara gaban ta, domin kalubalantar matakin.
A gefe guda gwamnatin tarayya ta dage cewa a nata bangaren matakin ya haifar mata da ɗa mai ido, kuma don haka baza ta sauya ra’ayi ba.
Yanzu dai abin jira a gani shine yadda zata kaya a goben, dangane da batun tsohon kudin.
A wani labarin kuma: Wasu Kungiyoyi Sun Kaɗa Kuri’ar Goyon Baya Ga Buhari Da Emefele
Wata gamayyar kungiyoyin farar hula CSO a ranar Talatar nan, sun kada kuri’ar amincewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele kan manufar amfani da kudi ba a hannu ba.
Da take yabawa da aiwatar da wa’adin tsohon na Naira da aka sauyawa fasali, kungiyar ta bayyana cewa, manufar wani shiri ne da zai kawar da Najeriya gaba daya daga cin hanci da rashawa, da almundahana da kuma sayen kuri’u.