Gwamnatin Jihar Kaduna ta shigar da sabuwar kara kan jagoran mazhabar shi’a Sheikh Ibrahim Elzakzaky kan rashin ɗa’a da kuma karya doka.
Wannan kara na zuwa kasa kwana guda bayan da wata babbar kotu dake zama a Kaduna ta bada umarnin sakin Elzakzaky bayan doguwar zamansa a tsare hannun gwamnati.
Idan ba a manta ba dai a yayin zaman kotun da ya wakana a ranar Laraba, Alkalin kotun Mai Shari’a Gideon Kurada ya ce zargin da gwamnatin ta shigar kan Elzakzaky a wancan lokaci ba tabbata ba, kuma hasalima ba garkame mutum akan laifin da ba a tabbatar ba.
To sai dai a ranar Alhamis gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar da wata sanarwa dake watsi da wancan hukuncin kotu inda ta ce ba ta gamsu kwata-kwata.
Lauyan gwamnatin Jihar Kadunar Dari Bayero ya tabbatar da cewa babu makawa gwamnatin za ta sake shigar da ƙarar Elzakzaky don tabbatar da gaskiyar abinda tun farko take zarginsa da aikatawa.
Tuni dai kamar yadda rahotanni suka tabbatar, Elzakzaky da mai dakinsa Zeenat suka shilla birnin tarayya Abuja don duba lafiyar su bayan da suka gaza samun jirgi zuwa kasar waje sakamakon yanayin lokaci.