Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta yi hasashen cewar da yiwuwar annobar cutar Korona ta hallaka ‘yan Afrika dubu dari da Hamsin idan har shugabannnin kasashen ba su tashi tsaye ba wajen dakile yaduwar cutar.
Har wala yau WHO ta ce; akalla mutane miliyan 200 annobar korona za ta kama a Afirka a cikin shekara guda.
Kwararrun da suka gudanar da binciken an wallafa ne a Mujallar BMJ Global Health, inda suka yi hasashen raguwar masu harbuwa da cutar a yankin fiye da sauran sassan duniya kamar Turai da Amurka, da kuma mutane kalilan da ke mutuwa.
Sai dai sun yi gargadin cewa duk da matakan da kasashen Afrika da dama ke dauka wajen kare kawunansu daga annobar cutar, amma rashin ingantattun ma’aikatun lafiya ka iya haifar da cikas wajen cimma nasarar yakin na su.