Juventus na nazari kan ɗauko tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino domin ya maye Maurizio Sarri a matsayin kocin kungiyar.
A wani labarin kuma, Manchester City na dab da kammala cinikin ɗan wasan baya na Bournemouth da Netherlands Nathan Ake, mai shekara 25.
Haka zalika, Manchester United ta yanke shawara kan farashin fam miliyan 80 ga ɗan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20.