Wani mai sharhi kan lamuran sufirin jiragen sama, Kaftin Alex Nwuba, yace a kwai yiyuwar wasu ƙarin Kamfanonin jirgen sama guda uku su dakatar da ayyukan nan da karshen wannan shekarar saboda matsalolin da fannin ke fuskanta.
Nwuba, wanda shine shugaban kungiyar masu jiragen sama da matuƙa jiragen ta kasa, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da gidan Telebijin na Trust TV.
Ya kara da cewa kokarin dawo da Kamfanin Jiragen Sama na ƙasa wato Nigerian Air, da ake kokarin yi ba zai yi wani tasiri ba wurin fuskantar kalubalen da ake fama da shi a bangaren jiragen sama.
KARANTA WANNAN LABARIN: Peter Obi Ba Ya Goyon Bayan IPOB—Baba Ahmed
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ɓangare jiragen sama na fama da matsalar tashin farashin man jirgi da ake kira Jet A1, da kuma tashin farashin kuɗaɗen waje.
A halinda ake ciki yanzu , kamfanonin jiragen saman kasashen waje guda biyu na Aero da “Dana” sun dakatar da ayyukan su na dan wani lokaci, lamarin da ya shafi harkokin zirga-zirga jiragen sama na duniya, yayin da sauran kamfanoni ke ci gaba da fadi tashi.
A wnai labarin kuma na daban.
Peter Obi Ba Ya Goyon Bayan IPOB—Baba Ahmed
Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Datti Baba-Ahmed, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi, ba ya goyon bayan kungiyar dake fafutukar kafa kasar Biafra wato (IPOB) da ayyukanta.
Baba-Ahmed ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana a shirin Daily Politics na gidan talabijin na Trust TV a ranar Litinin.
“Ban yarda da cewa Peter Obi yana goyon bayan IPOB ba saboda ba zan kasance tare da shi ba a yau (idan yana goyon bayan su),” in ji shi.
Ya lura cewa wadannan zarge-zarge ba su da tushe balantana makama.
Ya ce, “irin hirar da suka yi da ni lokacin da na ce ina so a yi min magana a zaben 2023 a matsayina na dan Najeriya. Babu wani abu da mutane ba za su iya cewa ba. A safiyar yau, dole ne in yi taron manema labarai don yawan labaran karya a duk faɗin duniya … waɗannan zarge-zargen har yanzu ba su da tabbas.”
Baba-Ahmed ya kara da cewa kafin ya amince ya zama abokin takarar Obi, ya yi duk binciken da zai iya kuma babu abin da ya danganta tsohon gwamnan jihar Anambra da kungiyar IPOB.
Ya ce, “Misali, sun ce an yi wa ’yan Arewa rashin adalci ta hanyar sanya katin shaida, kafin na yanke shawarar shiga tafiyar Peter Obi. A cikin makonni na yi duk binciken da zan iya. Tuni dai wayoyin hannu na dauke da kyamarori, na nemi har ma na bayar da diyya ‘ko zan iya ganin hoton wanda ya tsaya ya ce lokacin da Peter Obi yake gwamna a jihar Anambra, ga wani abu da yayi na goyon bayan IPOB, Wannan ya sanya ni na saka wannan?’ .
“Kuma bai kamata in zauna in yi imani da mutanen da ba su da hankali ba, saboda suna magana ko ta yaya kawai saboda kun fito siyasa lokacin da kowa ya san irin siyasar da akeyi a kasar nan.”