Ana alakanta dan wasan gaba na Chelsea Romelu Lukaku da komawa abokiyar hamayyarta Tottenham dake Birnin Landan domin haduwa da tsohon kocin Inter Milan Antonio Conte, in ji Jaridar Gazzetta Dello Sport.
Dan kasar Beljiya yana cikin rikici bayan ya bayyana cewa yana son komawa Italiya kuma baya son salon wasan Thomas Tuchel a wata hira da kafofin watsa labarai na kasar Italiya.
An fitar da dan wasan mai shekaru 28 a cikin ‘yan wasan da Chelsea ta buga ranar Lahadi kafin su tashi 2-2 da Liverpool ranar Lahadi.
Kungiyar ta ce za ta duba bacin ran Lukaku a Stamford Bridge tare da magance duk wata matsala da yake da ita a ciki kankanin lokaci.
Gazzetta Dello Sport ta ruwaito cewa Lukaku na iya tilasta komawa Tottenham don komawa wurin tsohon kocinsa Conte, wanda ya lashe gasar Scudetto a karshen kakar wasa ta 2020-21.
Lukaku ya koma Kungiyar Blues ne kan fam miliyan 97.5 a bazara kuma ya zura kwallaye bakwai a wasanni 18 da ya buga a bana.