Paris Saint-Germain a shirye take ta mayar da Thomas Tuchel a matsayin kocinta, a cewar RMC.
Daily Post ta ruwaito cewa, Christophe Galtier yana fuskantar matsin lamba a filin wasa na Parc des Princes yayin da kungiyar ke cikin wani hali.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bana Lokaci ne na Kirista ya mulki Najeriya – Gbagi
An yi imanin Zinedine Zidane shine babban wanda PSG ke so don maye gurbin Galtier, amma Tuchel kuma na da magoya baya a cikin kungiyar.
Har yanzu tsohon kocin na Chelsea ba ya aiki bayan da Todd Boehly ya kore shi a watan Satumba.
Tuchel ya kasance mai horar da PSG na tsawon shekaru uku, kafin shugaban kungiyar Nasser Al-Khelaifi ya kore shi a jajibirin Kirsimeti na 2020.
A wani labari kuma, Bana Lokaci ne na Kirista ya mulki Najeriya – Gbagi
Dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP a jihar Delta Olorogun Kenneth Gbagi, ya ce lokaci ne na Kirista daga yankin kudancin Najeriya ya samar da shugaban kasar na gaba.
Da yake magana a Asaba, a lokacin da ya fito a shirin ‘The Platform’ wani shiri na kungiyar ‘yan jarida ta kasa, NUJ, Gbagi ya ce ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi da na jam’iyyarsa ta SDP, Mista Adebayo. Adewole ne kadai ya cancanci tsayawa takarar shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabrairu