Al-Hilal na fatan zawarcin Lionel Messi daga Paris Saint-Germain a wannan bazarar, ta hanyar kulla yarjejeniya da takwarorinsa na Barcelona Sergio Busquets da Jordi Alba. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
An yi imanin cewa kungiyar ta dake buga gasar Saudi Pro League ta gabatar da kudin da ya kai fam miliyan 400 ga Messi, wanda ke shirin zama wakili na kyauta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Guda Cikin Jam’iyyu Ta Janye Kararta Akan Zababben Shugaban Kasa
Ba a tsammanin kyaftin din Argentina zai kulla sabuwar yarjejeniya da PSG.
A cewar El Chiringuito, Messi ya shirya karbar tayin Al-Hilal.
An kuma yi ikirarin cewa dan wasan da ya lashe kofin duniya Busquets zai amince da kwantiragin shekaru biyu a kungiyar dake Gabas ta Tsakiya idan kwantiraginsa ya kare a Barcelona.
Kazalika ana tsammanin Jordi Alba ma zai bi sahun yan wasan.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Uwargidan Tsohon Kakkakin Majalissar Dattawa Ta Rigamu Gidan Gaskiya
Jane Nnamani, matar tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Cif Ken Nnamani ta rasu. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
A cewar majiyoyi, ta rasu ne ta na da shekaru 60 bayan fama da jinya sanadiyar wata karamar tiyata da aka yi mata a Enugu.