- Tsarin zai magance ƙorafe-ƙorafen da wasu suke yi
- Buhari yana matuƙar bi da kiayey doka
- Buhari yafi Obasanjo sauƙin kai
Ministan ayyuka na ƙasa Chris Ngige ya bayyana cewa da za’a yi amfani da kundin tsarin mulkin Abacha da ya samar a shekarar 1995 da lallai an samu daidaito a ɓangarori da dama a ƙasar nan.
A yayin da yake hira da gidan talabijin ɗin Channels tv a ranar Litinin, ministan ya bayyana cewa tsarin mulkin yin wa’adi ɗaya na tsawon shekara biyar ga ko wane ɗaya daga cikin ɓangarori shida da ake dasu a ƙasar nan, shine zai magance ƙorafe-ƙorafen da wasu suke yi.
“Ina da yaƙinin kundin tsarin mulkin Abacha na 1995 wanda zai baiwa kowanne yanki damar riƙe shugabancin ƙasar na tsawon shekara biyar shine zai kawo maslaha akan irin matsalolin da aka fuskanta a can baya na yaƙin basasa da sauran su.”
Karanta wannan: An cire sunan mai tsaron gidan Manchester United daga gasar Euro

Ngige yace idan akayi hakan to kowanne yanki zasu ɗana shugabancin, kuma da yanzu maganar korafin da ƴan yankin kudu maso gabas keyi na cewar an ware su ya kau.
Ministan yace Buhari yafi tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo sauƙin kai, kamar dai yadda jaridar Dailytrust ta wallafa.
“Shugaba Buhari yana bin dokar ƙasa sau da ƙafa, ko kaɗan baya san karya doka, yana matuƙar tsoronta kuma yana kiyaye ta, fiye da yadda nake kiyaye ta.”
Ya ƙara da cewa shugaba Buhari yana haƙuri sosai da ƴan ƙasa, inda ya bayyana cewa Obasanjo bazai bari ana yi mishi irin wannan izgilancin ba.
A wani labarin kuma, jami’an yan sanda a Jihar Katsina sun cafke wani yaro dan shekara 13 busa zargin hallaka wasu yan fashin daji biyu a Jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa yaron mai suna Abdulkareem Mati a baya ya kasance yana yiwa gawurtaccen dan fashin dajin nan Ardo Nashaware aiki, a wani gandun daji Birnin Magaji dake Jihar Zamfara.
Kakakin rundunar yan sandar Jihar Gambo Musa ya shaida cewa jami’an nasu sun cafke yaron ne bayan ya tsere daga gandun dajin da ya ailata kisan.
Sai dai Mati ya bayyana cewa an dauke shi ne da zummar zai taimaka wajen kiwon shanu, amma aka karkatar da hankalinsa zuwa sarrafa bindiga kirar AK47 tare da maida shi mai kula da mutane da aka yi garkuwa da su.