- Jam’iyyar PDP a jihar Zamfara ta bukaci kotu da ta tsige Matawalle da mataimakinsa
- Tsige Gwamnan da mataimakinsa zai ba hukumar INEC damar gudanar da wani zaben, a cewar PDP
- A makonnin da suka gabata ne Gwamna Matawalle na jihar Zamfara ya sauka sheka zuwa APC, lamarin da ya jawo rikici a jihar
Jam’iyyar adawa ta Peoples’ Democratic Party (PDP) ta bukaci wata kotu gwamnatin tarayya da ke da zama a Abuja da ta yi amfani da karfin ikonta wajen tsige gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle da kuma mataimakinsa, Mahadi Aliyu Gusau.
PDP ta gabatar da wannan bukatar ne sakamakon sauya shekarar gwamnan da mataimakinsa daga jam’iyyar su ta PDP zuwa jam’iyyar APC, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Wadanda su ka shigar da ƙarar suna iƙirarin cewa, la’akari da hukuncin kotun koli da ta yi akan jam’iyyar APC na cewar ba ta da dan takarar gwamna a zaɓen jihar Zamfara na shekarar 2019 sakamakon gaza gudanar da zaben fitar da gwani, to zai zama karya doka idan Matawalle da Gusau suka ci gaba da kasance a mukamai alhalin sun koma APC, yin hakan kamar sun miƙa nasarar zaben ne daga PDP zuwa APC.
Daga cikin bukatun da suka gabatarwa kotun akwai, tilasta Matawalle da Gusau su yi murabus daga mukamansu don baiwa hukumar INEC damar gudanar da sabon zabe, a cikin watanni Uku, da kuma baiwa PDP damar sauya wasu da za su maye gurbin su.
A ranar Litinin bayan kammala sauraron jawabin lauyan masu karar, Kanu Agabi (SAN), mai shari’ar Inyang Ekwo ya bayar da izinin bin diddigin tsarin karbar kujerun gwamnan da mataimakinsa.
Cikakken labarin yana zuwa…
A wani labarin makamancin wannan, Mataimakin gwamnan jihar Zamfara Mahdi Aliyu Gusau, ya sami cikakkaken goyan baya daga jam’iyar PDP cewa, da ya kwace kujeran Gwamna Bello Matawalle.da ya kwace kujeran Gwamna Bello Matawalle.
Hakan na zuwa ne, biyo bayan sauya shekar Gwamna Matawalle zuwa Jam’iyar APC Mai Mulki, tun a ranar 29 ga watan Yuni shekarar nan.
DDUBA WANNAN LABARIN: Kotu ta yi barazanar cafke tsohuwar ministar jiragen sama, Stella Oduah da mutane 8
Matawalle da wasu zababbun masu rike da kujerun siyasa a jihar, sun bar jam’iyar adawa ta PDP, inda Mataimakin Gwamnan ya tsaya ya ki fice wa, inda ya ce, baya tare da wannan tsarin.
Idan za’a iya tunawa dai Mataimakin Gwamnan da Matawalle sun Sami nasaran hawa kujerar ce, a ranar 24 gawatan Mayun shekarar 2019, bayan Kotun Kolin, ta kwace nasarar da jam’iyar APC ta samu, bisa kama dan takaranta da sabawa tsarin zabe
Kazalika lokacin yanke hukuncin, Mai shari’an ya ce, dukkannin Yan takaran da suka tsaya a Jam’iyar PDP, su ne su kayi nasara a kafatanin zaben.
Rundunar Yan sandan jihar Zamfara ta toshe yunkurin Mahdi Aliyu Gusau, na kokarin kwace kujeran Gwamnan jihar, lamarin da ya sanya Jam’iyar PDP mai da martani a jiya Lahadi.
Mai magana da yawun jam’iyar PDP Kola Ologbondiyan, ya yi Allah wada da yunkurin jami’an yan sanda, na abun da ya kira, yunkurin dakile ikon da Mataimakin gwamnan ke da shi.