Daga Mu’azzam Yakubu Sanka
Shugaban Hukumar Korafe-Korafe da yaki da Al’mundahana ta Kasa Reshen Jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya Ce dukkan Korafe-korafen da ke Gaban su da zaran sun kammala Binkice Sukan mika shi ne ga Hukumar Shari’a domin Bayyana a gaban Kuliya.
Ya cigaba da cewa Yanzu haka akwai Batun Wasu Kudade da suka Haura Naira Miliyan Goma da Hukumar ta ke Binkicen su a Gidan Namun Dawa na Jihar Kano, Wanda aka Ce sun Bace ko kuma an dauke koma dai menene Binkice zai bayyana mana su, inji shi
Ya Kara da cewa mafi yawan Korafe-korafen da ke Gabanmu yanzu na wadanda aka kawo mana korafi ne da kuma Wanda muka shiga domin tabbatarwa ko akasin haka.
Kazalika abinda wasu basu sani ba game da Binkice shine Zargi daban Tabbatar da shi kuma daban in aka Ce ana zargin ka kan abu kaza Dan haka zo ka kare kanka a kai, Dan Me za ka ki zuwa? Binkice fa aka ce.
Shi yasa muke Kokarin wayar da kan Al’umma su fahimci Yadda dokoki suke kuma wannan yaki da muke yi da Al’mundahana Muna iya kokarin mu wajen saka Idon Basira da kyau domin Rairaye Karya da gaskiya.
Shugaban ya cigaba da cewa Muna Maraba da Kungiyoyi Masu zaman kansu wadanda ke Son ji daga garemu na irin aikace-aikacen da muke yi ko muka yi a baya, domin Hukumar mu a tsaye take kyam domin Tabbatar Gaskiya da Adalci.