Tsohon Sanata Mai wakiltar Plateau ta Tsakiya, kuma tsohon Mataimakin Shugaban majalissar Dattijai wato Sanata Ibrahim Nasiru Mantu ya rasu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gobarar Tankar Mai: Mutum 2 Sun Mutu, Motoci 14 sun kune a Anambra
Majiyar jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, Mantu ya rasu ne da sanyin safiyar yau talata, 18 ga watan Ogustan shekarar 2021.
Akwai Karin bayani……
A wani labarin Kuma, makamancin wannan..
Yanzu-Yanzu: Dan majalissa a inuwar jam’iyar PDP ya rasu
Wani Dan majalissar dokokin tarayya dake wakiltar mazabar Akure ta Kudu da Akure ta Arewa, Mai suna Mr Adebayo Omolage Wanda akafi sani da “Expensive” ya mutu.
Rahotanni sun bayyana cewa, Omolafe Dan majalissa ne daya lashe zabe a inuwar jam’iyar PDP, ya rasu ne da musalin karfe biyu na safiyar yau Litinin, a gidan shi dake Babban Birnin Tarayya Abuja.
Jami’in yada labarai na jam’iyar adawa ta PDP Kennedy Peretei ne ya tabbatar wa da Jaridar Dimokuradiyya rasu war dan majalissar.
Ya ce, “Kwarai Dan majalissar ya mutu ne a garin Abuja da safiyar yau Litinin, Kuma muna daf da sakin wata sanarwa akan hakan” inji shi.
An zabi Omolafe a zaben shekarar 2019, a karkashin inuwar jam’iyar PDP domin ya kwakillci yankin Akure ta Arewa, da kuma ta Kudu, a majalissar dokokinta Tarayya, bayan ya kwashe tsawon lokaci, ya na neman kujerar, tun daga lokacin da ya ke kan kujerar karamar hukumar Akure ta Kudu a shekarar 2009.