Akalla mutane 15 ne aka kashe a lokacin da ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyen Hayin Kanwa da ke unguwar Yakawada a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna a ranar Lahadi.
Lamarin ya faru ne kwanaki uku bayan da aka ce an kashe kimanin mutane 50 a kauyuka tara na karamar hukumar.
Wani ma’aikacin hukumar ‘yan banga na Kaduna (KADVS) a garin Giwa da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewa an yi jana’izar wadanda suka mutu a yau Litinin.
Ya ce al’amura na kara ta’azzara a Giwa saboda a kullum ana kashe mutane tun daga ranar Alhamis din data gabata
“Al’amarin ya yi muni saboda wasu ‘yan bindiga sun kashe karin mutane 15 a Hayin Kanwa a daren jiya Lahadi. Tun ranar alhamis wadannan ‘yan bindigar suke kai hari kauyuka suna kashe mutane,” inji shi.
Wani mazaunin Giwa mai suna Ridwan, ya shaida wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa ‘yan bindiga sun kai hari kauyen.
“Sun shigo kauyen suna harbe-harbe, wanda ya kai ga mutuwar wadannan mutane. Kun san cewa ba za a iya kwashe gawarwakin ba har sai da safiyar yau?” Yace.
Ya kuma kara da cewa ‘yan bindigar sun fi sha’awar kashe mutane fiye da sace su Ahalin yanzu.
Kazalika Wani mazaunin garin ya shaida wa wakilin Jaridar Daily Truat cewa an binne wasu daga cikin wadanda abin ya shafa a Tashar Sharri da ke kusa da garin Hayin Kanwa, ya kara da cewa adadin wadanda suka mutu na iya karuwa.
Ba a samu samun shugaban karamar hukumar Giwa Abubakar Shehu ta wayar tarho ba.
Kwamishinan tsaro da kula da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan bai amsa kiran waya da kuma amsa sakonnin tes da aka aika masa ba.
Kiran da aka yi wa jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Jalige Mohammed, shi ma bai amsa ba, inji Jaridar Daily Trust.