Daga cikin Mata 100,000, dubu 1,549 ke mutuwa wurin haihuwa a Bauchi — Inji Ɗan Takarar Gwamnan APC
Dan Takarar Gwamnan Jahar Bauchi a Jam’iyyar APC Air Marshall Saddique Abubakar ya bayyana baƙin ciki na yawaitar mutuwar mata a Jahar, yana mai zargin cewa mata 1,549 daga cikin 100,000 idan sun zo haihuwa, mutuwa suke yi
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Legas Na Shirin Kafa Hukumar Anti Okada a Jihar
Tsohon Hafsan Sojin Saman Najeriya ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da Ƴan Jarida a Bauchi.
An dai ayyana Abubakar a matsayin wanda ya lashe zaben fidda Gwani bayan ya samu nasarar samun Ƙuri’u 370 akan abokanan takarar sa guda 6.
Ya bayyana baƙin ciki na yawaitar yaran da basa zuwa makaranta a jahar yana mai nuni dacewar, kashe 29.9 suke zuwa Makaranta a Jahar, yana mai bayyana mamakin sa na matasa marasa aikin yi a Jahar, “dole a samu hanyar da za’a ɗauke su aiki”.
Dayake jawabi akan abinda yake so yayi domin kawo canji, tsohon Hafsan Sojin “ina so in Tabbatar ma kowa cewa zamu shigar da kowa. Akan magance matsalolin dake fuskantar al’ummar mu a yanzu.