• Mutum uku sun mutu a a wani asibintin Yara dake garin Ilorin din jihar Kwara,
• Ana kyautata zaton cewar sun mutu ne bayan sun ci Amala.
• Tun da fari dai Mutum biyar ne suka cinAmalan kafin daga bisani akaisu asibitin.
Mutum uku yan gida daya sun mutu a jihar Kwara, bayan sun ci abinci Mai dauke da guba.
Ana kyautata zaton cewa, wadanda lamarin ya shafa sunci Amala ne, a rukunin gidaje na Staple dake cikin karamar hukumar Ilorin na jihar.
Rahotonni sun nuna cewar, Mutum biyar ne dai yan gida dayan, su ka ci abinci mai dauke da guba, kuma a ka dauke su zuwa asibitin Yara na Igboro, inda an ne Mutum uku suka mutu hai lahira.
Wannan na zuwa ne kimanin wata guda, bayan makamancin lamarin ya afku, inda ake zargin an sanya wa, wani abinci guba a yankin Baruteen da Kaiama dake karamar hukumar Kwara ta Arewa, inda akalla mutun 17 ne a ke kyautata zaton sun mutum.
Koda aka tuntubi Mai magana da yawun Rundunar tsaron kaddarorin gwamnatin da kare al’uma wato NSCDC Babawale Zaid Afolabi ya ce, Bai sami rahoton faruwar lamarin ba.
Amma Shugaban cibiyar bincikin cututtuka da alalomin su DSNO Alhaji Muhammad Abdullahi ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce, Mutum biyu sun tsallake rijiya da baya.
Ya ce ” Mun ziyarci wurin da lamarin ya faru, kuuma Mahaifin su ya ce mana, Yara biyar ne su ka ci Amalan, Amma uku daga ciki, su kafara amai, kafin ayi gaggawar kai su asibiti Yara dake garin Ilorin.” Inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari Zai kaddamar da layin Dogo daga Kano zuwa Kaduna
Ya kara da cewa, ” Lokacin da mukayi kokarin ceto rayuwar su, sai daya ma ya fara aman, inda aka kai shi wata asibitin, Amma Mutum ukun farko sun mutu daga bisani.” a cewar shi.
” Mahaifin yaran Wanda manomi ne ya ce, da kanshi yake noma Doyar da ake yin Fulawar Amalan da ita, kuma bazai iya bayyana yadda lamarin ya faru ba” kamar yadda Jami’in ya bayyana.
Shugaban na DSNO ya ce, biyu daga cikin yaran yanzu haka suna nan cikin koshin lafiya.