Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama, kuma jigo a masu goyan bayan, dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC Bola Tinubu, ya ce gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ruguza jam’iyyar adawa ta PDP.
Lauyan kare hakkin dan Adam ya bayyana haka ne ta hanyar wani sako da ya wallafa a dandalinsa na sada zumunta a lokacin da yake mayar da martani ga ficewar Wike a kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ina Kalubalantar PDP Da Ta Dakatar Da Ni Daga Jam’iyyar – Wike
Wike, a wata zantawa da ya yi da wasu zababbun ‘yan jarida a Fatakwal a ranar Juma’a, ya sha alwashin ba zai ja da baya kan bukatarsa ta shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, wanda a halin yanzu ke barazana ga rarrabuwar kawuna a jam’iyyar.
Da yake mayar da martani, FFK ya ce rikicin da ke faruwa a jam’iyyar PDP zai share wa tsohon gwamnan Legas, Tinubu hanyar lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Ya rubuta, “Wike ya ruguza PDP. Ya ce Atiku ba ya da gaskiya, ba abin dogaro ba ne, ba shi da amana, kuma mayaudari ne. Ya ce Ayu mai cin hanci da rashawa ne, mai girman kai, mai nuna wariyar launin fata, mai son mulki, mai adawa da kudu.”
“Ya ce PDP na son mayar da ’yan Kudu bayi. Ya fasa kwallansu. ABAT shine shugaban mu na gaba!”
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Sace Jami’an ‘Yan Sanda Da Rana Tsaka
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da jami’an ‘yan sanda uku a Wasinmi da ke karamar hukumar Ewekoro a jihar Ogun.
Wakilinmu ya tattaro cewa an yi awon gaba da mutanen da suka ziyarci jihar Ogun daga shiyya ta 2, Onikan a jihar Legas domin gudanar da bincike, da rana tsaka.