Gwamnatin tarayya ta ce shirinta na ciyar da ‘yan makaranta dake Firamare zai ci gaba daga ranar Litinin din 14 ga watan Mayun 2020 a Abuja daga nan kuma shirin zai fadada zuwa jihohin Legas da kuma Ogun.
Hajiya Sadiya Umar Farouq, ministar jinkai da tallafi ita ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da Salisu Dambatta, mai ba ta shawara kan harkokin yada labarai ya fitar a ranar Talata a Abuja.
Ministar ta ce za su ci gaba da bada abincin ne sakamakon umurnin da shugaban kasa ya bayar.