Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed, ya umurci cibiyoyin gargajiya a jihar da su nemi amincewar gwamnatin jihar kafin bayar da mukaman gargajiya.
“An umurci dukkan Sarakuna da Manyan hakimai da dagatai a Jihar da su nemi izini daga Gwamnatin Jihar a hukumance kafin a ba wa kowa mukamin gargajiya,” Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da Zailani Bappa, mai ba shi shawara na musamman kan harkokin jama’a yada labarai da fadakarwa ya fitar ranar Larabar nan.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da Sarkin Birnin ‘Yandoto na karamar hukumar Tsafe, Aliyu Marafa, saboda ya ba wani “shugaban ‘yan bindiga, Ado Aleru mukami.
Wannan ci gaban bai yi wa galibin al’ummar ciki da wajen jihar dadi ba.
Sanarwar ta ce umarnin ya zama dole domin a duba mukamin da ake samu da kuma yiwuwar cin zarafin cibiyar gargajiya.
“Daga yanzu babu wani sarki ko babban Hakimi ko dagaci da zai nada kowa a wani ofishin gargajiya ba tare da samun izini da amincewa daga gwamnatin jihar ba.” Gwamna Matawalle ya ba da umarnin.
“Biye da wannan umarnin a yanzu ya zama tilas kuma rashin yin hakan zai jawo tsawatarwa daga gwamnatin jihar,” in ji gwamnan a cikin sanarwar.