Daga yanzu gwamnatin tarayya bata da hurumi wajen ƙayyade kuɗin farashin Mai, domin daga yanzu ‘yan kasuwa ne zasu ke ƙayyade yadda Farashin Mai zake kasancewa.
Hukumar ƙayyade farashin mai ta ƙasa PPPRA tace daga yanzu bata da hurumin ƙara yanke farashin mai, ta bar komai a hannun ‘yan kasuwa.
https://dimokuradiyya.com.ng/farashin-ɗanyen-mai-ya-karye-bayan-ragin-da-saudiyya-ta-yi/
Sakataren hukumar Abdulkadir Saidu ya ce “Daga yanzu matakin da muka ɗauka na daina ƙayyade farashin mai zai fara aiki nan take, domin yanzu kasuwar mai ce zata ke bayyana yadda mai zai kasance”.
Sannan ya ƙara da cewa hukumar tasu ba zata sake shiga lamarin da ya shafi ƙarin farashin mai ba, face ‘yan kasuwa da yanayin yadda ɗanyen mai yake a kasuwar duniya.