Wata budurwa ƴar Najeriya ta janyo cece-kuce bayan ta wulaƙanta saurayinta saboda ya nemi aurenta a gaban mutane.
A wani ɗan gajeran bidiyon da jaridar Legit.ng tayi kaciɓus da shi a Facebook, an nuna budurwar cikin coci lokacin da take murnar zagayowar ranar haihuwarta, inda mutane da dama suka taru a wajen.
KU KARANTA KUMA: Abun a yaba: Sanata Uba Sani yayi wata kyauta mai tsoka ga wasu ƙungiyoyin taimakon al’umma
Daga bayanta, kawai wani saurayi wanda ake kyautata zaton saurayinta ne ya duƙa ƙasa rike da zobe a hannun sa.
Budurwar tana waigowa kawai sai abun ya ɗaure mata kai, inda ta mayar masa da martani wanda bai taɓa zato ba.
Yayin da masu kallon su, suka yi ta cewa “ki amince”, budurwar sai ta tilasta saurayin nata ya miƙe tsaye.
Ta caccake shi bisa neman aurenta da yayi inda take mamakin dalilin da ya sanya ya zaɓi ya zubar mata da ƙima a gaban mutane.
Kafin yayi aune kawai, sai budurwar ta sharara masa mari a fuska, sannan ta watsa masa (cake) ɗin da take murnar zagayowar ranar haihuwarta da shi.
A daidai wannan lokacin ne mutane suka yi ƙoƙarin shiga tsakanin masoyan guda biyu, domin kada lamarin ya wuce gona da iri.
Bayan an fitar da saurayin daga wajen, budurwar ta gayawa mutanen dake tare da ita a wajen cewa, duka alaƙar su ta wata uku ce sannan ita bata son neman aurenta da yayi.
Ikon Allah: Bidiyon Yadda Mahaifiya Ta Ƙi Karɓan Jaririn Da Ta Haifa
A wani labarin na daban kuma, wata mahaifiya ta ƙi karɓan jariran da ta haiho, ta bayyana dalilan ta.
Masu amfani da shafukan sada zumunta sun mayar da martani sosai kan faifan bidiyon wata sabuwar uwa da ta ki taba jaririn ta inda ya jawo cece-kuce.
A cikin wani faifan bidiyo mai ban tausayi, wata ma’aikaciyar jinya ta mika mata jaririn a asibiti amma ta ki taba jaririn nata.
Duk da kokarin da ma’aikaciyar jinya ta yi na ganin ta dauki jaririn nata, matar ta ki, har ma ta kau da kai