Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano
Fitacciyar jaruma a Masana’antar fina-finan Hausa Kannywwod Hajiya Saratu Gidado wadda aka fi sani da Daso ta bayyana mamakin ta Kan yadda a ke tsangwamar ‘yan fim musamman mata alhalin Kuma sana’a su ke yi kamar yadda sauran Mata masu aikin Ofis da kasuwanci su ke yi.
Jarumar ta bayyana Hakan ne ga wakilin Dimukaradiyya in da ta ke cewa. “Ni a matsayina na’ yar fim Kuma da aure mijina Kuma ya ba Ni damar na cigaba da sana’ar da na ke yi a matsayin ‘yar fim, don haka Ina yin sana’a ta ne kamar yadda Mata masu aiki su ke yi.”
Ta Kara da cewar “Amma me ya sa idan’ yar fim ta yi aure ta cigaba da sana’ar ta ta fim sai a rinka kallon ta kamar ba ta da aure? Ai mu ma sai a rinka yi mana kallon kamar Mata masu yin akin su da sana’ar su a gidan mijin su. Mata nawa za a aure su, suna aiki Kuma su cigaba da aikin su.?
To in dai ana kallon su a matsayin Matan aure da su ke aiki to mu ma ‘yan fim idan mu na da aure mu ka cigaba da sana’ar mu ai ba wani abu ba ne in dai za mu kiyaye mutuncin auren mu ko a na so ne duk inda Mace take ko a gida ko a waje ta kiyaye mutuncin Kan ta da na auren ta don haka a daina yi mana wani irin kallo na daban. “