Afirka ta Kudu na gudanar da atisayen soji na hadin gwiwa da Rasha da China wanda ‘yan adawa suka ce ya nuna amincewar kasar da mamayar da Rasha ta ke yi a Ukraine. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Amurka ta kuma soki atisayen sojan ruwa na kwanaki 10, wanda za a ci gaba da gudanar wa domin bikin tunawa da yakin Ukraine na farko.
Sai dai gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce ba ta da hannu a rikicin, kuma tana gudanar da atisayen ne tare da wasu kasashe ciki har da Faransa da Amurka.
Atisayen sojan ruwa da ake kira Mosi, wanda ke nufin “hayaki” a yaren Tswana, na gudana ne a tekun Indiya da ke makwaftaka da gabar tekun Afirka ta Kudu.
Rundunar tsaron kasar Afirka ta Kudu (SANDF) ta ce dakarunta 350 ne za su halarci wannan gagarumin atisayi.
Kasar Rasha ta sanar da tura jirgin yakinta na Admiral Gorshkov mai dauke da makamai masu linzami na Zircon.
A wnai labari kuma, Da Yuwuwar Tuchel Ya Koma Tsohuwar Kungiyarsa
Paris Saint-Germain a shirye take ta mayar da Thomas Tuchel a matsayin kocinta, a cewar RMC.
Daily Post ta ruwaito cewa, Christophe Galtier yana fuskantar matsin lamba a filin wasa na Parc des Princes yayin da kungiyar ke cikin wani hali.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bana Lokaci ne na Kirista ya mulki Najeriya – Gbagi