• Dalibai 2 na makarantar Bethel Baptist dake Kaduna sun shaki iskar Yanci bayan tsrewa daga hannun Yan bindiga.
• Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna ASP Jalige ne ya tabbatar da wannan cigaban.
• Sai dai sama da Dalibai dari na hannun Yan bindigan a tsare.
Biyu daga cikin daliban Makarantar Sakandaren Bethel Baptist da a ka yi garkuwa dasu a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna, sun shaki iskar yanci.
An kubutar da daliban ne a garin Rijanna da ke kan babban hanyar Kaduna zuwa Abuja a yammacin jiya Laraba.
Lokacin da ya ke karin haske kan samun wannan cigaban, Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna ASP Mohammed Jalige ya ce, an kai daliban biyu zuwa wurin kula da lafiya na rundunar yan sanda, domin duba lafiyar su.
Daya daga cikin daliban da suka kubuta daga hannun yan bindigan an same shi ne, a cikin wani daji a makon jiya, baya ga dalibai sama da dari na tsare a hannun yan bindigan.
KARANTA WANNAN LABARIN: El-Rufa’i ya baiyana Dakta Danjuna Barde. Matsayin Samar da zaman lafiya
Kazalika idan ba a manta ba dai, masu garkuwan sun bukaci da a biya su naira milliyan sittin, a matsayin kudin fansa, kafin sakin daliban.
Comments 1