Hukumar lura da jarabawar NBAIS ta saki sakamakon jarabawar watan Yuni/Yuli na 2019 da daliban manyan makarantun karantar harshen Larabci da addinin Musulunci suka rubuta.
Farfesa Mohammed Abdulahi, mukaddashin magatakardar hukumar, shi ne ya tabbatar da hakan a ranar Talata a Kaduna a wata ganawa da ya yi da manema labarai.
A cewarsa, dalibai 36,141 suka rubuta jarabawar a duk fadin kasarnan, inda dalibai 28,645 suka yi nasara a yayin da dalibai 7, 496 suka fadi.
Ya tabbatar da cewa hukumarsu za ta yi iya bakin kokarinta wajen wayar da kan wadansu makarantun gaba da Sakandare da suke ganin cewa wadanda suka rubuta jarabawa a hukumar a bangaren kimiyya ba za su iya karatu a makarantar gaba da Sakandare da sakamakon ba. Sai dai ya tabbatar da cewa; suna da bayanai da ke nuni da cewa; dalibansu da suka rubuta jarabawa a hukumar sun shiga makarantu a cikin Nijeriya da ma wajenta da sakamakon kuma suna nuna kokari sosai a bangaren kimiyya.
Ya tabbatar da cewa hukumar ba kawai ta takaita karatunta ga bangaren addinin Musulunci da harshen Arabiya bane.