By Ishaq Dabai
Dalibai talatin da aka sace daga Kwalejin Gwamnatin Tarayya dake Birnin Yauri a jihar Kebbi sun samu ‘yanci.
Wannan na zuwa ne watanni hudu bayan da ‘yan bindiga suka kai hari makarantar suka yi garkuwa da dalibai da malamai da ba’a bayyana adadinsu ba, inda aka kai harin a cikin watan Yuni.
Yahaya Sarki, wanda shi ne mai bada shawara na musamman kan harkokin yada labarai ga gwamna Atiku Bagudu na Kebbi, ya tabbatar da sakin daliban a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
“A yau Alhamis, 21 ga watan Oktoba 2021, dalibai talatin (30) na Kwalejin Gwamnatin Tarayya dake Birnin Yauri sun isa Birnin Kebbi, bayan sakin su yayin da ake ci gaba da kokarin ganin an sako sauran da suke hannun ‘yan bindigar.” a cewar sa.
Sannan yace“Za a yi musu gwajin lafiya da tallafi yayin da zasu sake haduwa da danginsu. Muna gode wa duk wadanda suka taimaka wajen ganin an sako mutanen, yayin da suke taya Shugaban kasa, Muhammadu Buhari murnar samun nasara.”
Indan za’a iya tunawa jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A ranar 17 ga watan Yuni, gidan talabijin na Channels ya ba da rahoton harin da aka kai makarantar inda a lokacin maharan suka kashe dan sandan dake gadin makarantar.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Kebbi, Nafi’U Abubakar, ya yi karin haske cewa duk da maharan sun kai harin ne ta hanyar amfani da motar da aka sace daliban inda yace motar ba ta ‘yan sanda ba ce kamar yadda aka yi ikirari da farko.
Da yake karin haske kan yadda lamarin ya faru, ya ce ‘yan bindigar sun yi amfani da wata mota kirar Hilux mai lamba KBSJ 29 wajen isar da wadanda abin ya shafa.
“Bayan Shafe Kwanaki 10, Sun dawo daidai wannan yanki kuma sun shiga mazaba dake makwabtaka da wasu kauyuka, kuma sun yi aikin fiye da sama da awanni bakwai, suna bi gida-gida, daki zuwa daki, suna tara kudi, wayoyi, shanu, da duk wata na’ura da suke ganin tana da amfani ga ayyukansu, kuma sun bar sako a baya cewa nan ba da daɗewa ba za su dawo.
“Don cika alkawarinsu, jiya, muna da bayanan sirri cewa suna kan hanyarsu ta zuwa. Da misalin karfe 10:30 na safe, sun isa inda suka nufa-Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Birnin-Yauri. ”