Daliban Jami’ar Lagos sun gudanar da zanga zangar lumana domin nuna bacin ransu da kasa warware rikicin dake gudana tsakanin malamansu na karkashin kungiyar ASUU, da gwamnatin tarayya, abin da ya haifar da yajin aikin watanni sama da 3.
Daliban wadanda suka yi gangami a kan hanyar Hebert Macauly dake Lagos, kana suka yi tattaki zuwa makarantar tare da rakiyar jami’an ‘yan sanda suna dauke da allunan dake dauke da rubuce rubucen da suke bukatar gaggauta kawo karshen yajin aikin.
Daya daga cikin shugabannin daliban Yinka Alabi ya bayyana wa manema labarai cewar alhakin yajin ya rataya ne a wuyar gwamnatin tarayya wadda ta mallaki jami’o’in saboda haka ya dace ta dauki duk matakan da suka dace wajen sasantawa da malaman.
Alabi ya ce sun gaji da zaman gida, kuma akasarin su shekaru na dada kama su, yayin da suke daukar shekaru 5 zuwa 6 kafin kammala karatun shekaru 4 saboda yaje yajen aikin.
Shi kuwa Wani dalibi Mai suna Segun Adeyemi ya ce abin takaici ne kasar dake ikrarin neman ci gaba irin Najeriya na wasa da harkar ilimi wanda shine ginshikin ci gaban da ake samu a kowacce kasa.
Kana wata daga cikin masu zanga-zangar Mai suna Elizabeth Obinna wadda ta ce yajin aiki ya lalata karatun jami’a a Najeriya, ta zargi ‘yan Siyasar kasar nan, da gazawa wajen kare martabar ilimin yaran talakawa saboda ‘yayan su ba sa karatu a jami’oin, inda ta bukaci yin dokokin da za su tilasta wa jami’an gwamnati sanya ‘yayan su a irin wadannan jami’oi domin ba su kwarin gwuiwar kare martabar jami’oin a ko da yaushe.
Ita dai kungiyar malaman jami’o’in ta sanar da kara wa’adin ci gaba da yajin aikin har zuwa lokacin da gwamnati zata aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla
Kana dalibai daga manyan makarantun jihar Edo sun toshe kofar shiga filin jirgin sama na Benin da ke kan titin Airport Road domin nuna rashin amincewarsu da tsawaita yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in ta kasa ASUU ta yi na tsawon watanni uku masu zuwa.
Zanga zangar nasu ya tilasta wa masu ababen hawa sauya hanyyoyi zuwa wasu hanyoyin na daban.
Daliban da suka yi zanga-zangar sun hada da na Jami’ar Benin; da na Ambrose Alli University, da kuma na kwalejin kimiyya da Fasaha ta .Edo
Comments 1