Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin d’aukar dubban dalibai don basu horon zama manoman zamani, nan da shekaru goma masu zuwa.
Babban daraktan hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA) Kashifu Abdullahi ne, ya shaida hakan a taron karawa juna sani kan inganta sha’anin aikin gona daga tushe, wanda aka gudanar a Jami’ar Tarayya dake garin Dutse, a jihar Jigawa, yana mai cewa tsarin zai tallafa wajen rage zaman kashe wando.
A dangane da hakan ne, Jaridar Dimokuradiyya ta zanta da Farfesa Abba Garba Gaya na tsangayar aikin gona dake Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta jihar Kano kan alfanun shirin.
DUBA WANNAN LABARIN: Mata A Kasar Saudiyya Sun Fara Sana’ar Tukin Taxi Sakamakon Tsadar Rayuwa
”Wannan shiri zai taimaka Matuka musamman a wannan lokaci da muke ciki, da kuma halin da matasan mu suka tsinci Kansu.”
Daga nan, ya bukaci masu ruwa da tsaki dasu yi taka tsan-tsan wajen d’aura wad’anda zasu tafiyar da shirin, duba da yadda akan samu bata gari da kan yi uwa da makarbiya wajen Hana ruwa gudu.
A baya dai, gwamnatoci da dama, sun yi irin wannan yunkuri, amma kuma rashin mayar da hankali ya gaza haifar da ‘da mai ido, har Kawo wannan lokaci.
Comments 1