Dalibai 6 da Malamai 2 na Kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli dake Zaria, sun shaki iskar Yanci daga hannun masu Garkuwa da mutane.
An dai saki wadanda a kayi garkuwa da su din ne, a daran jiya Alhamis a wani yanki da ba’a san ko ina ne ba, dake jihar Kaduna.
Jami’in Hulda da jama’a na Kwalejin Abdullahi Shehu ya tabbatar wa da Gidan Talbijin na Channels wannan cigaban da aka samu. Inda ya ce, Dalibai da Malaman da a kayi garkuwa dasu a kwalejin, sun shaki iskar Yanci, bayan Yan uwa da abokan nan arzikin su, sun tattauna da Yan bindigan da su kayi garkuwa da su
Sai dai, bai ce komai ba,dangane da cewa, ko Yan uwan, sun biya kudin fansa ko a’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kungiyar G7 ta tallafawa Naijeriya da Makudan Kudade
.
Ya kara da cewa, Mahukunta makarantar zasu tarbi Daliban da Malaman a yau, a wurin da aka aje su bayan sakin na su.
Idan za’a iya tunawa dai, Yan bindigan sun afka Kwalejin ne a ranar 11 ga watan Yuni shekarar 2021 da muke ciki, inda su ka yi garkuwa da wadanda lamarin ya shafa a dakunan kwanan su dake Makarantar.
Inda a nan ne suka harbe wani dalibi har lahira, da kuma jikkata guda.