Shugabar jami’ar Benin, Farfesa Lilian Salami, a ranar Laraba, ta ce hukumar gudanarwar jami’ar a shirye ta ke ta bude makarantar don ci gaba da karatu, kuma hukumar ta tanadi dukkanin wasu matakan kariya daga cutar COVID-19.
Ta ce jami’ar za ta tabbatar da cewa kowanne dalibi, malami da ma’aikaci zai kiyaye dokokin COVID-19 domin dakile bulla da yaduwar cutar a cikin makarantar.
Shugabar jami’ar ta bayyana hakan ne a zantawar da gidan talabijin na NTA a shirin Barka da Safiya Nigeria, wanda kuma jaridar The Punch ta cire labarin.
Salami ta ce wasu daga cikin dalibai sun fara yin barazanar dukan malaman su ma damar aka ci gaba da kulle makarantun kasar.
KARANTA WANNAN: Gasar Firimiyar Najeriya: Kano Pillars za ta kara da Plateau United
Tun dai a matan Maris 2020 ne daliban makarantun gwamnati ke zaune a gida tun bayan da kungiyar Malaman Jami’o’i ASUU ta shiga yajin aikin da ya kwashe watanni 9.
Sai dai, kungiyar ta janje yajin aikinta a ranar 24 ga watan Disamba 2020, bayan da aka sha kai ruwa rana tsakaninta da gwamnatin tarayya.
Duk da hakan, a lokacin da dalibai ke murnar shirin komawa makarantun, sai kuma kasar ta sake fadawa cikin annobar COVID-19 karo na biyu.
A baya bayan nan kwamitin dakile cutar COVID-19 da fadar shugaban kasa ta kafa ya umurci makarantu su ci gaba da zama a kulle har sai ranar 18 ga watan Janairu 2021.
Sai dai kungiyar ASUU ta jaddadata cewa har yanzu makarantu ba su da karfin dakile yaduwar cutar, don haka bai kyautu a bude makarantun ba.
A nata jawabin, shugabar jami’ar UNIBEN ta ce hukumar makarantar ta za ta yi duk mai yiyuwa don tabbatar da kiyaye dokokin COVID-19 a cikin makarantar.