
- Daliban da aka kwashe a yawuri sun dawo gida a yau.
- A yammacin Juma’an nan ne Gwamnan Jihar kebbi yake bayyana dawowar daliban da Malaman gidanau.
- A ranar Alhamis data gabata ne Yan bindiga sukai awon gaba da dalibai da malamai da dama a makarantar.
KARANTA:- Gwamnan Jihar Ogun Abiodun yakai ziyara shagunan da wuta ta kone
Gwamanan Jahar kebbin ya bayyana dawowar daliban ne a yammacin yau Juma’a inda jami’an tsaro suka dawo dasu.
Gwamanan dai Jim kadan bayan aukuwar lamarin ya bayarda umarnin daukan matakin gaggawa don ganin an kubutar da daliban da Malaman.
Anyi musayar wuta tsakanin sojojin da Yan bindigar lokacin da ake kokarin kubutar da daliban.
A lokacin da ake kokarin kubutar da daliban da Malaman anyi arangama da barayin bayan da jami’an tsaro suka fatattako su tun daga yawuri zuwa Riyao zuwa garin Samba, a lokacin ne Yan bindiga suka rabu gida biyu wasu suna kora daliban da Malaman wasu Kuma suna kora sharu.
Nwachuku ya bayyana cewar ” sojojin kasa gami da na sama ne sukai gamin gambiza wajan kwato rayan inda suka farama yan bindigan Aman wuta misalin karfe 2:30.
A lokacin, sojojin sun dawo da shanu kimanin 800 inda suka ce zasu cigaba da bin diddigin Yan bindigan har sai sunje inda suke Tara mutane don kwato su.
Sojan yace za’a damka daliban da Malaman wajan Gwamnatin Jihar kebbin.
A wani labarin:- Ƴansandan jihar Kebbi sun ƙaryata zargin da ake yi kan cewa ƴan bindiga sunyi amfani da motar su wajan kwashe Ɗalibai da Malamaishe Ɗalibai da Malamai.
Ƴan sandar jihar Kebbi sun ƙaryata zancen dake yawo kan cewar ƴan bindiga sun yi amfani da motar ƴan sanda a lokacin da suka sace Ɗaliban 50 na Makarantar Yawuri dake Kebbi.
A cewar Nafi’u Abubakar ɗan sandan yace motar da ƴan bindiga sukai amfani da ita sun ƙwace tane wajan wani babban Alƙali dake Kebbi tare da rubutun “Kebbi State Judiciary” Mai lamba KBSJ 29.
Ya ƙara da cewa hukumar ƴan sandan zasu cigaba da bayyana lamarin akai akai.
Ya cigaba da cewa ƴan sandan zasu ƙulan ƙawance da sauran takwarorinsu don tabbatar da kuɓutar waɗanda aka sace.