Daga Abdullahi Kebbi
Daliban kasar jamhuriyar Nijar sun gudanar da zanga zangar neman gwamnati ta kori sojojin kasar waje daga kasar tare da inganta harkar ilimi a dukkan fadin kasar.
Daliban sun bukaci sojojin kasashen Amurka, Faransa, dakuma Jamus da su bar kasar, suna kuma yiwa sojojin Nijar Addu’a, inda suke nuna alluna dake dauke da Rubutu mai taken ” Allah ya daukaka sojojin Nijar” ” Allah ya tsinewa sojojin kasar waje”.
Sai dai akwai bayanai dake nuna cewa an gudanarda irin wannan zanga-zanga a wasu garuruwa na jamhuriyar ta Nijar.