Daliban Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure sun tsayar da zirga-zirgar mutane da ababen hawa, sakamakon hare-haren da wasu bata gari ke kai musu a kullum.
Daliban da suka gudanar da zanga-zangar sun tare hanyar Akure zuwa Ilesha babban titin, wanda hakan ya haifar da cunkoson ababen hawa.
Daliban sun ce zanga-zangar ta zama wajibi domin bayyana kokensu ga jama’a
Kokarin da hukumomin tsaro suka yi na bin diddigin lamarin ya ci tura yayin da daliban suka ki amincewa da shiga tsakani na ‘yan sandan Najeriya.
Tsohon shugaban kungiyar daliban makarantar, Abram Ezebede, ya ce wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka addabi daliban.