By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Larabar data gabata ne aka kai wa wasu mazauna unguwar Agbowo da wasu titunan dake makwabtaka dasu hari tare da jikkata su yayin da wasu ‘yan fashi da makami suka kai farmaki a gidajen kwanan dalibai masu zaman kansu da ke kusa da harabar jami’ar Ibadan.
Wakilinmu ya tattaro cewa ‘yan bindigar da suka kai farmaki a yankin Barika da titin Agricola da kuma unguwar Agbowo da ke karamar hukumar Ibadan ta Arewa a Ibadan, sun bindige wasu dalibai tare da sace wayoyin tarho, iPad, kwamfutar tafi-da-gidanka da sauran na’urori masu dauke da kaya da kuma kudi.
Wasu daga cikin daliban sun shaida wa wakilinmu cewa ‘yan fashi da makami sun iso ne da misalin karfe 1:30 na dare, inda har zuwa karfe biyun dare.
A Agbowo, an harbe wani mai gadin dare da wani dalibi mai suna Victor tare da jikkata shi.
An ce an kai dalibin zuwa cibiyar lafiya ta UI wadda aka fi sani da Jaja Clinic yayin da sauran wadanda suka jikkata aka kai su zuwa wani asibiti mai zaman kansa da ke yankin.
Wani dalibi mai suna Eddy, ya ce rashin tsaro a yankin Agricola ne ya sa aka samu nasarar yin fashin.
Sannan ya ce, “Na samu labarin cewa an kori jami’an tsaron da masu gidajen haya suka dauka a titin Agricola saboda matsalar biyan albashi.
’Yan fashin da adadinsu ya kai 12 sun zo ne dauke da bindigu,Injin yankan katako, wukake da sauran makamai.
“Sun tsallake katangar suka sauka a masaukinmu suka fara fasa kofa suna harbi don tsorata mu, Sun so mu san cewa suna dauke da makamai.”
An ce ‘yan sandan Sango da sauran yankunan sun yi gaggawar zuwa wurin amma ‘yan bindigar sun yi gaggawar ficewa kafin ‘yan sandan su iso.
Wani dalibin UI ya ce dalibai uku sun jikkata a masaukinsa amma babu wanda ya mutu.
Kazalika dalibin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce
“Wata ɗaliba ta rasa na’urori da yawa a tashin hankalin da suka hada da IPhone dinta suka dauke daga baya suka dawo suna tambayarta ta rubuta musu lambobin sirrin din manhajar din ta na banki.
“Ta yi sauri ta je ta duba asusunta inda taga cikin kudin, ta gano cewa sun share asusunta baki daya.”
Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso, bai amsa kiran da aka yi masa ta wayar tarho tare da sakon kartakwana da aka tura masa a wayarsa akan lamarin ba.