Sanata malam Uba sani tare da Gwamna El’rufa’i na jihar Kaduna sun karbi bakuncin dalibai yan asalin jihar Kaduna, dake Karatu kasashen waje.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wani sakon sa daya wallafa a shafin sa na sadarwa, inda Malam Uba Sani ya ce, “A yau, na kasan ce tare da jagoran mu, mai kaifin basira, gwamna Nasir Ahmad El -Rufai, da abar kaunar sa Kuma matarshi Hajiya Asiya El -Rufai da Babban mai ba gwamna shawara, Jimi Lawal, da Manajan Daraktan Kamfanin Ci gaban Kasuwanci na jihar Kaduna Hafiz, wajen karbar ɗaliban da suka samu tallafin Karatu a kasashen ketare, daga Gwamnatin Jihar Kaduna wadanda suka kawo ziyarar girmama wa a masaukin mu” inji Sanatan.
” Daliban da yanzu ke karatun digiri na biyu, wadanda suka kammala karatun digiri na farko a jami’o’in gwamnati a Najeriya, Kuma gwamnatin jihar Kaduna ta zabe su, domin ci gaba da karatun su a jami’o’in kasashen waje, a matsayin wani yunƙuri da sanin yakamata, don haɓaka ƙwazon ma’aikatan jihar tare da aiki da ilimi” kamar yadda ya bayyana.
KARANTA WANNAN LABARIN: An kashe Manoma biyar a jihar Osun
“Daliban da suka ba da labarin abubuwan da suka samu tare da Gwamnan, inda Kuma na ke yaba masa, kan yadda ya ba su wannan dama da ba kasafai ake samu ba, duk domin samun ilimin da zai sa su jera kafa’da da kafa’da da kasashen duniya.” Inji shi.
Kazalika Sanata Uba Sani ya cigaba da cewa, “Sun yi alƙawarin bayar kansu ga jihar kaduna, bayan kammala karatun su. Gwamna El-Rufa’i ya yaba musu sakamakon kyawawan halayen su a cibiyoyin karatun, sannan ya dora musu nauyin kula da karatun a kan su, da kansu” a cewar shi.
Comments 1