By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Kano ta ce jihar ta samu nasarar kashi 95 cikin 100 a jarabawar hukumar shirya jarabawar ta kasa (NECO) a shekarar 2021, inda sama da dalibai 80,000 suka sami maki tara.
Kwamishinan Ilimi na jihar Alhaji Sanusi Sa’idu-Kiru ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai kan nasarorin da ma’aikatar ta samu a shekarar 2021.
Ya ce jihar ce ta fi kowacce yawan ‘yan takara da suka zana jarrabawar kammala sakandare (SSCE) a kasar nan.